Yaki Da Cutar Shan Inna A Najeriya

wata ma'aikaciya tana raba maganin rigakafin shan inna

Kaddamar da rigakafin cutar Shan inna a dukkan yankunan Arewacin Najeriya idan aka ‘dauke jihar Kwara, na gudana ne ta hanyar ‘daukar matakan kula da zirga zirgar yara ta kan iyakokin kasar.

Rigakafin dai na wuni Hudu da za a kammala ranar Talata mai zuwa, na samun karancin cikas a wasu yankunan jihar Yobe dake farfadowa daga yankin Boko Haram da kuma daman yankin Goza na Borno inda aka samu bullar cutar bayan da bayan Najeriya ta ayyana cin nasara.

Babban jami’in yaki da Shan inna na ma’aikatar lafiyar Najeriya, Dakta Nasiru Sani Gwarzo, yace an haifi wasu yaran da basu taba ganin abin da ake kira allurar rigakafi ba a wasu yankuna, yanzu kuma anzo yanayin da amfara sakin wadannan gurare zirga zirga ta fara tabbata tsakanin cikin birane da wadannan lungunan, tabbas hakan yasa za a fara samun matsaloli da yaran suke fitowa da su.

Jami’ar lafiya matakin farko ta jihar Yobe, Dakta Hauwa Lari, tace akwai wadatar alluran rigakafin inda tace a wannan watan na Satumba suna shirin ga yara Miliyan Guda da Dubu 17 da 882, sun kuma shirya yin ta ne a tashoshi da kasuwanni da kuma mafitar Manyan garuruwa inda manayan motoci ke fita safara.

A dukkan aikin rigakafin dai Najeriya zata yi amfani da alluran rigakafi Miliyan 300, inda tun farko ta bayyana tana da Miliyan 100 a ‘kasa.

Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Ta Yi Nasarar Kawar Da Cutar Shan Inn A wasu Yankunan Da Boko Haram Ta Addaba - 2'58"