Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadan MDD Mai Kula Da Jin Kai Ya kai Ziyara Yankin Dake Fama Da Matsalar Tsaro A Nijar


Toby Lanzer Jakadan MDD Mai Kula Da Jin Kai A Kasashen Yankin Kudu Da Sahara
Toby Lanzer Jakadan MDD Mai Kula Da Jin Kai A Kasashen Yankin Kudu Da Sahara

A Jamhuriyar Nijar karamin Sakatare na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Ayyukan jin kai a kasashen yankin Kudu da Sahara, Toby Lanzer, ya kai wata ziyara a kasar wanda ya samu ganawa da al'ummar Diffa dake fama da matsalar tsaro.

Ziyarar na da nasaba da shirye shiryen babban taro na kasa da kasa kan tafkin Chadi, da za a gudanar ranar 19 ga watan Satumba a birnin New York na kasar Amurka. Toby Lanzer, ya samu kai ziyara ta gani da ido a yankin Diffa musamman ma a garuruwan Bosso da Tumur.

A wani taron manema labarai da ya kira a birnin Yamai ya bayyana damuwarsa game da halin da al'ummar Diffa ke ciki, inda yace abin da ya gani a yankin Diffa al’amari ne mai matukar ban tsoro game da abin da ya shafi tsaro.

Tony Lanzer, dai yace game da batun ‘yan gudun hijira na yankin Diffa wani bincike ya nuna cewa ana bukatar Dala Miliyan Dari Uku da Goma Sha Shida domin kulawa da su, to amma Miliyan Dari da Goma ne kawai kasashen duniya suka bayar a gidauniyar, al’amarin da ake gani tamkar kasashen duniya sun fara juyawa al’ummar Diffa baya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG