Tsohon Gwamnan jahar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya zargi shugaba Muhammadu Buhari a zaman shugaba wanda ya gaza kan aikinsa.
Bafarawa yace yayinda 'yan Najeriya suke fadin albarkacin bakinsu kan tsananin rayuwa, shi a nasa ra'ayin, babu mai laifi sai shugaban kasa domin tilas ne ya zamanto mai karbar shawara. Yace ya rubutawa shugaba Buhari wasiku domin neman ya ganshi ya bashi shawara, amma har yanzu bai sami amsa ba.
Bafarawa yace wannan musiba da aka shiga ta shafi kowa, ba tareda la'akari da jam'iyya ba. Saboda haka idan za'a shawo kanta, dole shugaba ya saurari kowa. Bafarawa wanda jigo ne a jam'iyyar 'yan hamayya watau PDP, ya zargi 'yan arewa da tsuke bakunansu kan matsalolin da gwamnatin Buhari take fuskanta. Yace idan shugaban yana jin ba'a zaginsa da gwamnatinsa, to zai sha mamaki, domin ana yi,don tsoro yasa ba'a gaya masa.
A martaninda ya bayar kakakin fadar shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya kwatanta maganar Bafarawa, da 'yan fashi da zasu shiga gida cikin dare su wawushe komi, sannan su komo da rana suna tambayar mai gidan cewa yaya aka yi ba shi da abinci a gidan.