Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nasarar Yaki da Cutar Ebola A Najeriya


Cutar da ta lakume rayuka dubu goma sha daya a kasashen Afirka ta Yamma
Cutar da ta lakume rayuka dubu goma sha daya a kasashen Afirka ta Yamma

Lokacin da cutar Ebola ta kunno kai a kasashen Africa ta yamma cikin shekarar 2014 ta shiga yiwa jamaar ta illa, Likitoci a Najeriya sun yi kokarin ganin sun dakatar da wannan cutar mai kisa cikin yan watanni.

Yau ana iya cewa wannan labari ya zame tarihi.

Lokacin da cutar ta shigo cikin birnin Ikko, birnin dake da mutane da yawan su yakai miliyan 20.

Cutar wadda ake iya yadata, ta hanyar cudanya da juna kuma ya zamanto cewa hakan wata babbar barazana ce domin ko mutane na yawan cudanya daga zuwa aiki har zuwa gida. A ko wane lokaci cikin turmutsitsi ake gudanar da harkokin yau da kullun.

Yanzu haka dai an samar da majigi akan wannan cutar, inda aka nuna yadda likitoci da jami’an kiwon lafiya suka yi ta kokarin ganin sun dakatar da yaduwar wannan cutar kafin bazuwarta zuwa kasar wadda tafi ko wace kasa yawa a nahiyar Africa.

Kuma sunyi nasarar hakan domin ko cutar ta kashe mutane takwas ne kacal daga cikin dubu 11 data kashe a yankin na Africa.

Wadda ta samar da wannan majigin Bolanle Austen Peter tace majigin yana nuna yadda yan Najeriya suke alfahari da wannan nasarar da suka samu.

XS
SM
MD
LG