Yaki Da Boko Haram: Matasa Na Namijin Kokari a Najeriya Da Makwabtan Kasashe - Inji Masana

'Yan Sa Kai

Kasashe makwabtan Najeriya sun fara gane tasirin rawar da matasan sa-kai da ake kira Civilian JTF ke takawa wajen karya lagon ‘yan Boko Haram al'amarin da ya sa tuni wasunsu suka fara fito da nasu tsarin, wanda hakan kuma ke matukar taimakawa

Biyo bayan sa hannu da matasan sa-kan Civilian JTF suka yi a fafatawar da ake yi da mayakan Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, masana sun ce hakan ya taka rawa wajen samar da kwanciyar hankali a wannan yankin.

Makwabciyar kasar Kamaru ita ma ta dauki wannan matakin. Alhaji Ceini, basaraken Crenewa a Kamaru, ya ce da kadan-kadan jama’ar gari suka fara bin tsarin amma yanzu suna kokarin aiki dare da rana don sa ido a gari.

Aboube Wargazen, shugaban hukumar ne a Diffa, ya ce su ma suna da jami’an sa-kan amma ba sa daukar makamai, sojoji kadai ke daukar makamai.

Ambasada Zanna Bukar Kolo, jakadan Amurka a kasar Chadi ya ce duk da cewa ana samun nasara da mayakan boko haram a wannan shiya ya kamata a sani yakin na da wuyar sha’ani.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Rawar Da Jami'an Sa-kai Ke Takawa a Makwabtan Kasashen Najeriya