Yadda 'Yan Bindiga Suka Kai Hari Sakkwato A Ranar Idi

.

Yadda ‘yan ta'adda ke nuna gadara wajen kai hare-hare ga jama'a, na tilas ta shugabannin al'umma jaddada kira ga hukuma da ta yi da gaske wajen shawo kan wannan matsalar.

Hare-haren ta'addanci dai kusan a ce yanzu lamarin ya kwancewa kowa kai domin yadda lamarin ke karuwa na hari ba daga ‘yan bindiga.

Harin da ‘yan bindiga suka kai wa al'ummar gabashin Sakkwato a garin Isa ranar sallah duk da yake ba’a samu salwantar rayuwa ko jikkata wani ba, a cewar shugaban karamar hukumar Abubakar Yusuf Dan Ali, abu ne mai nuna cewa akwai bukatar daukin gaggawa domin abin ya wuce da wuri.

Rundunar 'yan sanda ta jihar Sakkwato ta tabbatar da aukuwar kai harin da kuma jajircewar jami'an tsaro wajen korar yan ta'addar, sai dai kawo lokacin hada wannan rahoto, ba'a samu cikakken bayani daga jami'an da ke can yankin.

Muryar Amurka ta tuntubi wani mazaunin garin domin jin yanayin da ake ciki bayan jami'an tsaro sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar.

Karin bayani akan: ‘yan bindiga, jihar Sakkwato, Musulmi, Muryar Amurka, Nigeria, da Najeriya.

Lamarin rashin tsaron dai na ci gaba da jan hankulan jama'a musamman a arewacin Najeriya inda jagororin al'umma ke ci gaba da kiraye-kiraye ga gwamnati.

Mai alfarma sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar, na daga cikin masu wannan kiran.

‘Yan Najeriya dai na ci gaba da sauraren gwamnati ganin yadda za ta amsa wadannan kiraye-kiraye da jama'a ke yi, ko da za'a samu sauyi ga matsalolin na rashi tsaro.