Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa mayaka masu ikirarin jihadi masu alaka da kungiyar Al-Qaed da IS, sun hallaka dozin-dozin din fararen hula a Burkina Faso kamar yadda hukumomi suka tabbatarwa da AFP.
Wasu mahara ne suka kai wannan hari na baya-bayan nan a kauyen Barsalogho da ke tsakiyar arewacin kasar a ranar Asabar kamar yadda majiyoyi da dama suka tabbatar.
Ministan sadarwa Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo, ya kwatanta harin a matsayin “ragwanci” da wani “gungun masu laifi” ya kai.
“Maharan sun kaikaici mata, yara da tsofaffi inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi” Ouedraogo ya fadawa gidan talbijin na kasa.
Wani mazaunin yankin ya fadawa AFP ta wayar tarho cewa, an kai harin ne da misalin karfe 9 na safe a ranar Asabar.