Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Hadin Kai Da Tsaro Na A Gaba-Gaba A Babban Taron ECOWAS A Abuja


ECOWAS
ECOWAS

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin Afrika ta yamma da ake kira ECOWAS ta kammala babban taronta karo na 67 a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya tare da sake zaben , Shugaban Najeriya Bola Tinubu a matsayin mai jagorantar kungiyar.

Muhimman batutuwa da taron da shugabanni daga kasashe sha biyu suka halarta ya tattaunawa akai sun hada da tsaro, wanda yankin Afrika ta yamma ke fama da shi, lamarin da ya shafi harkokin cinikayya, tattalin arziki da bunkasar wadatar al’ummar yankin, a saboda haka ya zama wajibi kungiyar ta dauki duk matakan da suka dace don fitowa da hanyoyi ko dabarun magance matsalolin tsaro a yankin.

Bayan haka, akwai batun yadda za a fara aiwatar da kudin bai daya, a zaman wani bangare na bunkasa harkokin cinikayya da tattattalin arziki cikin sauki da walwala a tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

A jawabinsa a wurin taron, shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya jaddada muhimmancin tsaro da kuma hadin kan mambobin kungiyar, da duba matakan da za su kai ga taimaka wa juna, da kuma bunkasa tattalin arziki.

Shi ma wakilin tarayyar Turai, Muhamman Ibn Chambas, ya bukaci kasashen yammacin Afrika su hada kai, su fito da matakan bai daya, don tabbatar da yankin ya sami bunkasa.

Hakazalika, Ali Ture, Shugaban hukumar da ke gudanar da kungiyar ECOWAS, ya yi kira ga mambobin kungiyar da su fito da hanyoyin da zasu kai ga hadin kai, wanda a yanzu ake bukata sosai a yankin ganin irin rarrabuwar kawunan da aka samu, da hayanyar shugabanci da kuma matsin tattalin arziki.

Sai dai Ambasada Adamu Daura, mai sharhi kan harkokin diflomasiyya a Najeriya, ya bayyana damuwa akan yadda taron zai yi nasara ba tare da kasashen Niger, Mali da Burkina Faso ba, wadanda suka tabbatar da cewa sun fice daga kungiyar a daidai lokacin da ake neman hadin kan kowa da kowa don samun ci gaban yankin.

“An sami gibi babba a taron, saboda kashen Nijar, Mali da Burkina Faso da suka fita daga kungiyar, abin da ya kamata yanzu shi ne kungiyar ECOWAS ta yi kokarin maido da wadannan kasashe a cikinta don a sami hadin kan da ya dace" a cewar Daura.

A halin da ake ciki, shugabannin kungiyar ta ECOWAS sun sake zaben Shugaban Najeriya Bola Tinibu wani sabon wa'adin shugabancin kungiyar, sannan sun amince da matakan kafa rundunar kota kwana ta yaki da ta'addanci da kuma tsara takardar kudin bai daya ta ECOWAS.
Ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Tugga ya ce tun kafin a sake zaben, shugaba Tinubu ya jaddada cewa Najeriya ta amince zata taimaka wa ECOWAS da kudaden shiga don samar da rundunar ta tsaro da nufin yaki da 'yan ta'adda.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Umar Faruk Musa:

Batun Hadin Kai Da Tsaro Na A Gaba-Gaba A Babban Taron ECOWAS A Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG