Yadda Wasannin Cin Kofin Duniya Ke Gudana A Yau

Jerin sunayen kasashen da suka samu hayewa zuwa zagaye na goma sha shida, a gasar cin kofin duniya wadda yake gudana a kasar Rasha na 2018 acikin kasashe 32 da suke kece raini.

Da kuma kasashe wadanda basu samu zuwa zagaye na gaba ba. A wasan da akayi a ranar litinin 25/6/2018 a matakin wasan rukuni zagaye na uku, Uruguay ta lallasa masu masaukin baki Russia daci 3-0.

Saudi Arabia ta samu nasara akan Kasar Masar da kwallaye 2-1, Spain tayi canjaras 2-2 tsakanita da Morocco sai Iran sukayi kunnen Doki 1-1 da kasar Portugal. Kasashe shida ne suka samu hayewa zuwa zagayen gaba na gasar bayan kammala wasan ranar litinin kasashen sune kamar haka.

Russia mai masaukin baki Uruguay, France, Croatia, sauran kasashen sune England, da Belgium. Wadanda suka gaza zuwa wasan gaba kuwa sune Saudi Arabia, Egypt, Poland, Costa Rica, Tunisia, Panama, da kasar Morocco.

Inda ayau za'a cigaba da fafatawa a sauran wasannin domin zakulo sauran kasashen zuwa zagaye na 16 wasu kuma su koma gida. A yau kasar Australia zata kara da Peru, sai Denmark da France, da misalin karfe 3 agogon Kamaru da Chadi.

Nigeria zata fafata da Argentina sai Iceland da Croatia da misalin karfe bakwai agogon Najeriya Nijar Kamaru da kasar Chadi.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasannin Tamola A Ayu 2' 40"