Masu sha'awar kwallon kafar daga sassa daban daban na duniya musamman a nahiyar Afirka suna ci gaba da nuna farin cikinsu da kuma jinjina wa tawagar ‘yan wasan kwallon kafa na kasar Senegal, bisa bajintar da suka yi, ta samun nasara a wasan da suka yi da kasar Poland inda suka doke ta da kwallaye 2-1, a gasar cin kofin kwallon Kafa na duniya na 2018 wanda yake gudana a kasar Rasha.
Magoya bayan sun bayyana cewer ba shakka kasar Senegal ta fidda nahiyar Afrika kunya a gasar cin kofin duniya ta bana.
Kasancewar Senegal ce kadai daga cikin kasashe biyar masu wakiltar nahiyar Afrika wadda ta samu nasara a wasanta na farko a gasar cin kofin duniya da ke gudana bana a Rasha.
Magoya bayan dai sun bukaci Super Eagles ta Najeriya da kuma Tunisia da su yi koyi da takwarorinsu na Senegal wajen samun nasara a sauran wasannin da suka rage masu dan samun damar zuwa zagayen gaba haka kuma sunyi addu'ar Allah ba kasar ta Senegal nasara a sauran wasaninta.
Tuni dai aka yi waje rod da kasar Masar da kasar Morocco daga gasar sakamakon wasanni biyu duk an doke su, sai dai suna zaman cikon umurni inda ya rage masu wasa daya kacal wanda ko da sun samu nasara ba zai yi masu amfanin zuwa zagayen gaba ba.
A ranar Lahadi mai zuwa Senegal za ta fafata da kasar Japan, a wasanta zagaye na biyu daga rukunin (H) kasar Japan dai ita take jagorantar rukunin bayan ta lallasa Colombia daci 2-1, yayinda ita kuma Poland zata kara da kasar Colombia.
Facebook Forum