Wasu daga cikin manya manyan jami'an hukumar kula da wasan kwallon Kafa ta Najeriya NFF karkashin jagorancin shugabanta Amaju Pinnick sun yi wata tattaunawar surri tsakaninsu da tawagar ‘yan wasan Super Eagles tare da jagororinsu.
Ganawar anyi ta ne a Kaliningrad, dake kasar Rasha Jim kadan bayan rashin nasara da Najeriya, ta yi a wasanta na farko tsakaninta da kasar Croatia, a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya inda aka ci Najeria 2-0 a ranar asabar 16/6/2018.
Ta bakin wasu daga cikin shuwagabannin na NFF sunce hukumar ta bayyana wa ‘yan wasan cewar tana tare dasu duk da abunda ya faru sai dai bata bukatar faruwar irin wannan abun a sauran wasannin da suka rage.
A bangaren ‘yan wasan sun bada tabbaci ga hukumar cewar zasu samu nasara a wasan da ya rage masu na rukuni tsakanin su da Iceland da kasar Agentina dama wasu nan gaba.
Har ila yau Ministan matasa da wasanni na kasa Solomon Dalung ya shawarci mambobin hukumar da su dakartar da duk wani shirye shiryen zabe na shuganin hukumar da suke shirin yi har sai bayan gasar ta cin kofin duniya dake guda a yanzu inda tuni wasu suka fara kamfen naneman tsayawa takara.
Zaben dai zai gudana ne a watan Satumba yayinda wa'adin shugaban hukumar Amaju Pinnick ya kare tare da wasu jami'anta.
Facebook Forum