Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gasar Cin Kofin Kwallon Duniya Mafi Tsada A Tarihin Tamaula


Gasar cikin kofin kwallon kafa na duniya da ake kan gudanarwa a kasar Rasha “FIFA World Cup” an kiyasta cewar shine wasa da yafi kowanne tsada a tarihin cin kofin duniya. Wanda aka ware kimanin kudi wuri na gugar wuri dalar Amurka billiyan $15.

An kashe kimanin dala billiyan $3 wajen gyara da gina sabbabin filayen wasa “Stadium” haka aka kashe billiyan $8 wajen gyaran hanyoyi da samar da wasu sababbi, haka da gyaran hanyoyin jiragen kasa da tashoshin jiragen sama.

Abin tambaya a nan shine wannan me yake nufi ga mutanen kasar Rasha masu biyan haraji? A cewar Farfesa Leonid Grigoryev, na tsangayar bincike da tattalin arzikin kasa a kasar Rasha, gaskiya ana iya kwatanta wannan kashe kudin da kamar mutun ne ya sayi rigar auren sa mafi tsada.

Idan akayi la’akari da yadda aka kashe kudi a lokacin gasar cin kofin duniya da aka gabatar a Brazil, za’a ga cewar ba daya yake da na wannan karon ba, domibn kuwa Brazil sun dauki wasan kwallon kafa a matsayin babbar sana’a.

Amma muma muna bukatar hakan yazama wani abu da zamu cigaba ba kawai a sanmu da wasan kwallon hockey kawai ba, idan akayi duba da yadda kasar Brazil ta gudanar da wasan cin kofin duniya da ya gabata an kashe kudi kimanin dalar Amurka billiyan $11. Idan aka kiyasata baki daya kudin za’a ga cewar adadin kudin sun kai kimanin Naira Triliyan dari biyar da ashirin da biyar.

Ana sa tsammanin wannan wasan zai kara darajar kasar Rasha a idon duniya, duk kuwa da irin cin zalin da take yi a kasar Ukraine.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG