Rahotanni daga Najeriya na cewa, rundunar sojin kasar sun halaka akalla mayana Boko Haram takwas a jihar Neja da ke tsakiyar arewacin kasar.
Ko da yake, har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wani karin haske daga jami'an tsaro na Najeriya akan wannan al’amari da ya faru a ranar Lahadin da ta gabata.
Amma rahotanni sun tabbatar da cewa, baya ga mayakan da aka kashe, sojojin Najeriyar sun yi nasarar cafke wasu manyan kwamandojin kungiyar biyu.
Kwamishin kula da harkokin tsaron cikin gida na Jihar Neja Mr. Emmanuel Umar ya tabbatar da aukuwar lamarin sannan ya bukaci jama’a su baiwa jami’an tsaro hadin kai.
Shugaban karamar hukumar ta Borgu Hon. Ahmed Baba Suleiman Yumu, ya ce mayakan na Bok Haram sun kai hari ne da nufin kubutar da ‘yan uwansu dake kulle a gidan yarin barikin sojin sama dake Wawa ta yankin Kainji, amma sai sojojin Najeriya suka samu nasarar kawar dasu.
Ku Duba Wannan Ma Sojojin Saman Najeriya Na Cigaba Da Kai Farmaki Kan Mayakan ISWAPTuni dai gwamnatin Jihar Nejan ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankali domin ana daukar matakai akan lamarin kamar yadda sakataren gwamnatin Jihar Nejan Ahmed Ibrahim Matane ya bayyana mana.
Wannan al’amari dai yana zuwa ne kasa da mako daya da gargadin kasar Amurka ga Najeriya akan barazanar hare-haren ‘yan ta’adda a birnin Abuja fadar gwamnatin kasar dama wasu Jihohin da ke kusa da birnin na Abujan.
Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari
Your browser doesn’t support HTML5