Yadda Rufe Iyakokin Kasashen Afirka Ta Yamma Ya Haifar Da Tsadar Rayuwa A Nijar

Yadda masu manyan motoci suka danse hanya

Yadda masu manyan motoci suka danse hanya

Watanni sama da hudu bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar jama'a na ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa sakamakon karayar tattalin arziki tun bayan takunkumin da kungiyoyi irinsu ECOWAS ko CEDEAO suka lafta wa Nijar.

Watanni kusan biyar bayan hambarar da Bazoum Mohamed, al’ummar Nijar na ci gaba da kokawa kan tasirin takuntumin da kasashen yammacin Afirka suka kakaba wa Nijar.

Takunkumin da aka sanya wa Nijar ya kasance mai tsauri da aka taba sanya wa wata kasa mamba a kungiyar ECOWAS, inda kasashen yankin suka dauki matakin rufe iyakokinsu da soke duk wata alakar cinikayya da gwamnatin mulkin sojan Nijar.

Wannan mataki dai ya haifar da hauhawar farashin kayan bukatun jama’a na yau da kullum kuma ya haifar da koma bayan tattalin arziki a wasu sassan kasar. Al'umar Nijar sun yi kira da a tausaya wa talakawa duba da irin halin da suke ciki, saboda ba a taba ganin hauhawar farashin kayayyaki irin wannan ba.

Kungiyar 'yan kasuwa ta yi kira ga 'yan kasuwa da su tausaya wa talakawa, la'akari da halin da suke ciki a daidai lokacin da ake fuskantar karancin kayayyaki, lamarin da shi ma ya haddasa tashin farashin kayan a kasuwanni.

Aminou Waje, shi ne shugaban kungiyar 'yan kasuwa na jihar Agadas, ya bukaci 'yan kasuwa da su ji tsoron Allah, kada su kara farashi ta yadda talakawa za su kasa biya.

Kungiyoyin da ke yaki da tsadar rayuwa a Nijar irinsu ADDC wadata, sun yi kira ga jagororin mulkin sojan kasar da su tattauna da 'yan kasuwa domin sama wa al’umma mafita, kamar yadda Mohamed Aboubacar wakilin kungiyar ADDC wadata a Agadas ya bayyana.

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan girman takunkumin da aka sanya wa Nijar da ya yi sanadin tsadar kayan masarufi, lamarin da ke neman kara nisanta 'yan Nijar da abinci.

Saurari rahoton Hamid Mahmud:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Rufe Iyakokin Kasashen Afurka Ta Yamma Ya Haifar Da Tsadar Rayuwa A Nijar