Daruruwan mata ne suka yi dandazo a harabar ofishin wakilcin CEDEAO a Nijar a ranar Laraba 18 ga watan Oktoba da zummar nuna kosawa da takunkuman da kungiyar kasashen yankin na yammacin Afrika ta kakaba wa Nijar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatin dimokradiyya a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
Halin kuncin rayuwar da abin ya haddasa wa jama’a ya sa matan da ke kiran kansu Femmes Patriotes kiran kungiyar ta canza matsayi kamar yadda Malama Naomi Binta Stansley ta bayyana. Ta ce yara yanzu sun kasa zuwa makaranta saboda takunkumin.
Wakiliyar mata ma’aikatan asusun baitulmalin Tresor National, a wannan taro ta jaddada cewa sun fara daukar matakai don samar da kudaden gudanar da al’amuran hukuma ta hanyar kudaden shiga na cikin gida.
Wasu daga cikin mukarraban majalissar sojojin CNSP sun halarci harabar ofishin wakilcin na CEDEAO don karfafa guiwa ga masu wannan zaman dirshan. Colonel Ibro Amadou ya yi jawabi a madadinsu, inda ya ce yunkurin da su ke ta yi ya fara ba da sakamako.
Yunkurin jin ta bakin reshen ECOWAS ya citura domin in ban da maigadi babu jami’in kungiyar ko guda a ofishinta na birnin Yamai a halin yanzu. Wata majiya tace tun a washegarin takun sakar da ta kunno kai a tsakanin kungiyar da sojojin da suka yi juyin mulki ma’aikata suka daina zuwa ofis, watakila saboda dalilan tsaro.
Rufe iyakoki, da tsinke wutar lantarki, da kuma sanya takunkumi kan kudade da kadarorin Nijar na daga cikin tarin takunkumin da CEDEAO ta kakaba wa wannan kasa da zummar matsa lamba wa sojojin su mayar da shugaba Mohamed Bazoum kan kujerarsa. A makon jiya wasu matan dabam sun yi gangami a harabar reshen bankin bankunan kasashen yammacin Afrika wato BCEAO don nuna bukatar a mayar wa Nijar kudadenta da aka sanya wa takunkumi sanadiyar juyin mulkin.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna