Yadda Mutane Suka Fara Tunkarar 'Yan bindiga A Sokoto

A Najeriya alamu na nuna cewa jama'a sun fara debe tsoron ‘yan ta'adda domin suna bayar da gudunmuwa wajen kamawa ko kisan barayin, wanda kuma bai rasa nasaba da ganin cewa hukuma ta kasa magance matsalolin.

Alamu na nuna tura na dada kaiwa bango domin kuwa duk da yake barayi ‘yan fashin daji, dauke da muggan makamai suke ta’asar su, yanzu mutane suna fito na fito da su kuma suna samun galaba akan barayin wani lokaci tare da taimakon jami'an tsaro.

Irin hakan ya faru a garin Illela da ke jihar Sokoto a Arewa Maso Yammacin Najeriya inda rana ta batarwa masu satar mutane da suka shiga garin wanda ke iyaka da Jamhuriyar Nijar, ranar Lahadi ranar da kasuwar kasa da kasa ta garin take ci har suka sace wata mata da ‘yan'yanta maza biyu amma basu sha da dadi ba.

Yayin Santana da wani mazaunin garin malam Lawal wanda a gaban idonsa lamarin ya faru, ya ce wani abokinsa ne ya kira ya fito inda suka dinga jin harbe-harbe daga bisani suka ga wasu dauke da wata mata, kuma da mutane suka biyo su sai suka fada wani gida inda aka zagaye su aka hau kansu da taimakon wadanda ke cikin gidan.

Shi ma wani mazaunin garin ya ce dubu ce ta cika domin dama ana zargin mazauna wadannan rugaggen Fulani akan cewa ba su rasa masaniya akan ayyukan ta'addanci dake faruwa a garin na Illela.

Matsalar masu kyankyasawa barayin bayanai wadanda ake kira Informants a turance, ita ce wasu ke ganin ke kara rura wutar ayyukan na ta'addanci domin ko a makon da ya gabata gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya tauna tsakuwa domin tsoratar da masu wannan dabi'ar.

Mun nemi jin ta bakin rundunar 'yan sanda akan wannan batun amma dai kiran da muka yi wa kakakin rundunar ASP Sanusi Abubakar ya samu karbuwa ba.

Yanzu dai abin da aka zurawa ido a gani shi ne yadda za'a yi da informants da ake kamawa domin ko a makon da ya gabata an kama wasu a garin Goronyo kuma aka mika su ga jami'antsaro, musamman bisa ga furucin da gwamnan ya yi wanda kuma shi ne babban jami'in tsaro a jiharsa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda Mutane Suka Fara Tunkarar 'Yan bindiga A Sokoto