Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Yi Amfani Da Karfi Domin Murkushe Masu Kawo Tashin Hankali A Filato - Buhari


Shugaba Buhari (Twitter/ @BashirAhmaad)
Shugaba Buhari (Twitter/ @BashirAhmaad)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin amfani da karfi wajen murkushe masu ta da kayar baya a jihar Filato.

A cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya fitar, shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin tarayya na shirin daukar matakai na dakile tashe-tashen hankali a jihar Filato, tare da alkawarin yin amfani da karfi domin murkushe masu ta da kayar baya a jihar.

To sai dai kuma Buhari ya ce nasarar hakan ba za ta samu ba, ba tare da hadin kan al’ummomi a jihar ba.

“Dole ne al’ummomi su taru su haka kai waje yaki da munanan hare-hare, domin kuwa hare-haren ramuwar gaya ba shi ne mafita ba” in ji sanarwar ta shugaban kasa.

Haka kuma ya kalubalanci shugabannin addini da sarakunan gargajiya, da su ci gaba da yin kira ga zaman lafiya, su kuma kaucewa farfaganda da hura wutar rikici a tsakanin mabiyansu.

Ya ce ana nan ana karfafawa al’ummomin da ke fama da tashin hankali da karin jami’an tsaro, domin kariyar rayuka da dukiyoyin jama’a.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar ta Filato ta bayyana sassauta dokar hana fita ta sa’o’I 24, da aka mayar daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Gwamna Simon Lalong
Gwamna Simon Lalong

Jihar ta Filato dai ta sha fama da rikice-rikice a ‘yan kwanan nan, da ake ta’allakawa da addini da kabilanci.

XS
SM
MD
LG