Wasu ‘yan Najeriya na tunanin cewar ba lalle bane wannan ziyara ta sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ta yi tasiri ba, ganin wa’adin shugaban Amurka Barack Obama na dab da ‘karewa.
Kwararre kan harkokin diflomasiyya kuma tsahon jakadan Najeriya a kasar Sudan, Ambasada Sulaiman Dahiru, na ganin akwai banbanci kan yadda ake gudanar da harkokin kasashen waje a Amurka, kasancewar kowacce irin jam’iyya ce kan mulki to zata ci gaba da kudurin da aka riga aka tattauna tsakanin Amurka da sauran kasashe.
Shi kuma tsohon ministan harkokin wajen Najeriya, Dakta Aliyu Idi Hon, na ganin dole ne kasar kamar Najeriya, ta nemi zaman lafiya da yarda ga kasashe kamar su Amurka, wadanda suka ci gaba a duniya idan har ana son cimma bukatu irin na ci gaba da zaman lafiya da ma kwato kudaden da aka sace daga kasar.
Tsohon babban sakataren hukumar raya tafkin Chadi, Alhaji Baba Abba, na duba ziyarar ne ta fuskar alaka tsakanin Najeriya da Amurka. Inda yace hakan yana jaddada yarda da gwamnatin Amurka da mutanenta ke da shi ga gwamnatin Najeriya. wanda hakan zai kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.
Saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina daga Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5