Jami'in hulda da jama'a na rundunar DSP Othman Abubakar, ya yi gargadin ne biyo bayan kisan wani matukin keke Napep, mai suna Abba a garin Numan Wanda ya harzuka 'yan kungiyar matuka keke Napep su kayi zanga-zanga da katse babban titin Numan zuwa Yola da lalata ofishin kungiyar.
Wasu daga cikin dabaru da suke anfani da su akwai na siddaru da yaudarar biyansu makuden kudade haka kuma daga bisani su kashe su, su kwace keken.
Shugaban kungiyar matuka keke Napep na karamar hukumar Numan Pwati Ngiso, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce sun Kama wasu Dalibai biyu na kwalejin kimiya da fasaha na Numan da suke tuhuma da hanunsu a kisan, kuma suka mika su 'yan sandan yankin.
Wakilin Muryar Amurka Sanusi Adamu, ya yi hira da kawun Wanda aka kashe Malam Hassan, wanda ya nuna kaduwarsa da wannan kisan. Wani ganau ya fadi cewa 'yan fashin keken na yaudara su kaisu lunguna inda ba jama'a sannan su kashe su su dauki kekunan.
Saurari cikakken rahotan Sanusi Adamu.