Mr. Adamu Kamale dan majalisar wakilan Najeriya dake wakiltar mazabar Madagali da Michika, daya daga cikin yankunan da lamarin ya shafa, ya nuna fushinsa da lamarin dake faruwa.
Dan majalisar yace zasu bi digdigin batun amma ya soma ne da wasu yankunan da al'ummomi suka koma. Yace wasu kananan hukumomi guda bakwai maimakon a kai masu tallafin abinci sai a kai Yola a raba. Yace wadanda suke karban abincin a Yola ba 'yan gudun hijira ba ne, ba kuma wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita ba ne.
Yace tallafin abinci da aka tara walau daga gwamnatin tarayya ko kungiyoyin jin kai, kamata ya yi a bi lardi lardi ana rabawa ba a tsaya a Yola ba kawai. Yace yawancin abincin a kasuwar Yola yake shiga inda ake sayar dashi. Yace lamarin ya tayar masu da hankali.
Yace suna da labari tireloli saba'in da biyar aka tura zuwa jihar Adamawa amma ko tirela daya bata shiga cikin Michika da Madagali ba. Karkata abincin ya bar mutanesu suna fama da yunwa.
Yace zasu fara bincike ne ta bangaren gwamnatin jihar kafin su san matakan da zasu dauka.
Amma sakataren hukumar dake kai agajin gaggawa ta jihar Asema Haruna Hamaforo yace su a saninsu babu wani kayan tallafin da aka karkatar. Yace duk wani tallafi da ya shiga hannunsu, suna bin ka'ida wajen rabashi.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.