Ziyarar ta biyo wadda shi John Kerry ya kai kasar Kenya shekaranjiya kafin ya nufi Najeriya.
Ambassador Jibrin Tinade yayi tsokaci akan ziyarar musamman akan abun da yake hangowa kan irin moriyar da kasar zata ci a wannan ziyarar.
Yace duk ziyarar da zata karfafa zumunci tsakanin Najeriya da Amurka tana da kyau kuma zata kasance da alfanu musamman yanzu ma da Najeriya take da abubuwa da dama da ta sa gabanta. Wadannan abubuwa kuwa sun hada da tashin hankalin da Boko Haram ke haddasawa da sha'anin cin hanci da rashawa da kudaden kasar dake waje da kuma irin wahalar da al'ummomin jihohin Borno, Adamawa da Yobe suke sha.
Dangane da bukatun da Buhari zai gabatarwa John Kerry sai Ambassador yace ai ita ma Amurka tana da bukatu. Tace tana son ta tattauna da Najeriya akan yaki da ta'adanci a duniya gaba daya. Suna son su tattauna akan tattalin arziki da Najeriya. Kuma Najeriya zata so ta tattauna dasu akan wasu manyan batutuwa da suka shafi kasar da duniya.
Yace idan an bi maganganun Shugaba Buhari basu wuce batun tattalin arzikin kasa da samar wa 'yan Najeriya aikin yi da zaman lafiya musamman a yankin Niger Delta ba, kuma da neman taimakon yakar rashin zaman lafiya a arewa maso gabas da Boko Haram ke haddasawa.
Yace kasar tana bukatar taimako a samu zaman lafiya a Sudan ta Kudu da wasu kasashen Afirka da Amurka zata iya taimaka a shawo kansu.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.