Garuruwan da 'yan-bindigan su ka sakawa wannan haraji a yankin na Birnin Gwarin jihar Kaduna, sun hada da Unguwan Fari, Unguwan Makera, Unguwan Badewa, Unguwan Dan-Fulani, Sadauki da sauran garuruwan da su ka ce rashin mafita ya sa dole su ka ba da wadannan miliyoyi don tsira daga hare-haren 'yan-bindigan, kamar yadda daya daga cikin al'umar yankin ya shedawa manema labaru.
Kafin tattara wadannan miliyoyin kudin sasanci, wasu al'umomi a yankin na Birnin Gwari sai da su ka biya wasu miliyoyi ga 'yan-bindigan don samun damar killace kayan gonar da su ka noma.
Kuma daya daga cikin mazauna yankin ya ce biyan kudin ma ba lallai ne ya zama tsira ba.
Su dai mutanen da Muryar Amurka ta yi zanta da su a yankunan sun nemi da kada a bayyana sunayensu bisa dalilai na tsaro.
Duk kokarin jin ta bakin Kwamishinan tsaro na jahar Kaduna Malam Samuel Aruwan ya ci tura saboda ya ce suna wurin taron tsaro.
Sai dai daya daga cikin masu sharhi kan al'amurran yau da kullun, Barista El-zubair Abubakar ya ce wannan labari na da matukar hatsari ga tattalin arzikin al'uma da kasa baki daya.
Yankin Birnin Gwari mai kewaye da dajujjuka dai na kan gaba wajen fama da hare-haren 'yan-bindiga kamar dai yadda yankin Zangon Kataf ke fama a kudanchin jahar Kaduna don ko a jiya lahadi ma gwamnatin jahar Kaduna ta tabbar da kashe wasu mutane goma sha daya da 'yan -bindiga su ka yi a yankin.
Saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikra:
Your browser doesn’t support HTML5