Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC a Najeriya ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Imo kuma Sanata mai ci a yanzu Rochas Okorocha bisa zargin sama da fadi da kudaden gwamnati da suka kai Naira biliyan 2.9
Hakan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da tsohon gwamnan ya fito a hukumance ya ayyana niyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
Ana dai zargin Rochas da hada baki da wasu kamfanoni guda biyar da suka hada Naphtali International Limited, Perfect Finish Multi Projects Limited, Consolid Projects Consulting Limited, Pramif International Limited, da Legend World Concepts Limited tare da wani dan siyasa daga jam’iyyar APC mai suna Anyim Nyerere Chinenye wajen wawure kudaden cikin tuhume-tuhume 17 da hukumar ta EFCC ta shigar babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Litinin.
A zantawar da Muryar Amurka ta yi da shugaban hukumar EFCC Malam Abdulrashid Bawa, ya bayyana cewa tun ba yanzu ba hukumar ke bincike akan Rochas wanda aka ba da belinsa bayan tsare shi da ta yi.
Ya kara da cewa ko a watan Afrilu na shekarar 2019 sai da aka tsare shi na tsawon kwanaki biyu don amsa tambayoyi bisa zargin almundahana da kudaden gwamnati.
Ku Duba Wannan Ma Hukumar Ya’ki Da Cin Hanci Ta EFCC Ta Kama Shugaban Gidan Radiyon Muryar NijeriyaKazalika a watan Agustan 2019, sai da hukumar EFCC ta sake tsare Sanatan don amsa wasu karin tambayoyi bayan ta gano wasu kadarori da suka hada da gidajen zama, makarantu, da kasuwanni da dai sauransu dake da alaka da shi.
Daga cikin kadarorin da hukumar ta rufe a lokacin sun hada da makarantar Rochas Foundation College dake Owerri, East High Primary and Secondary School a Owerri wacce ‘yarsa ta farko mai suna Uloma Nwosu ke lura su da kuma babban katin siyayya ta All-In Supermarket a garin Owerri duk a jihar ta Imo.
Idan za’a iya tunawa gabanin lokacin zaben shekarar 2019 da ya gabata sai da hukumar EFCC ta tuhumi Okorocha bisa zargin fitar da sama da Naira biliyan 1 daga asusun gwamnatin jihar don taimakawa yakin neman zaben surukinsa Uche Nwosu, a lokacin zaben gwamnan jihar ta Imo.
lamarin da ya kai da Hukumar ta kuma kama Akanta-Janar na jihar, Uzoho Casmir, bisa zargin taimakawa Okorocha wajen cire kudaden
Sai dai a bangaren Rochas kuwa ya karyata zarge zargen da hukumar ta yi mishi a wata hira da gidan talabijin na Channels ya yi da shi yana mai cewa Maimakon a tuhume shi da laifin cin hanci da rashawa, shi ya kamata ya gabatar da kararsa na kin biyansa hakkokinsa a lokacin yana gwamna na tsawon shekaru takwas.
Ko da yake Okorocha ya bayyana cewa wannan ba shi ne karon farko da ya ke fuskantar irin wannan cin zarafi daga hukumar EFCC ba, yana mai cewa siyasa ce kawai da bita da kulli
Sai dai kuma tsohon gwamnan ya shawarci hukumar EFCC da kada ta bari ta zama makamin ‘yan siyasa amma ta binciki zarge-zargen sannan ta samu hakikanin gaskiya kafin daukar matakan da suka dace.