ABUJA, NIGERIA - Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu ya ce yada jita-jita a yanar gizo ya zama daya daga kalubalen da babban zaben Najeriya na 2023 zai fuskanta.
Farfesa Yakubu ya nuna takaicin cewa wallafa sakamakon zabe da irin wadannan kafafen ke yi na riga malam-masallaci na cikin abubuwan da kan haddasa fitina.
A nan shugaban hukumar zaben INEC a takaice ya nuna aniyar hukumar sa ta hada kai da kafafen yanar gizo da su ka san ya kamata a lamuran zaben don tallafawa yada labarun gaskiya.
Jami’a a sashen labarun hukumar Zainab Aminu ta ce “INEC na da kafafen da ta ke yada sahihan labaru a dukkan kafafen sada zumunat.”
Yakubu ya juya ta kan lamuran tsaro ya na cewa hukumomin tsaro sun ba da tabbacin samar da yanayi mai kyau gabanin lokacin zaben don gudanar da shi ba tare da cikas ba.
Shugaban na INEC ya ce aikin hukumar sa shirya zabe yayin da sauran hukumomi ke da na su bangaren na tsaro don kare lafiyar jami’an zabe da masu kada kuri’a.
Gabanin tafiyar sa Amurka, Farfesa Yakubu ya yi taro da manema labaru inda ya nuna goyon baya ga shawarar kafa kotu ta musamman da za ta rika hukunta wadanda kan take dokokin zabe.
Masu sharhi na cewa Najeriya na da dokoki masu kyau, amma ba su faye tasiri ba sai in a na bukatar tasirin na su.
Saurari cikakken rahoto dag Nasiru Adamu El-hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5