Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Za Ta Rufe Aikin Rijistar Zabe A Ranar 31 Ga Watan Yuli


Shugaban hukumar zabe ta INEC Farfesa Yakubu Mahmood
Shugaban hukumar zabe ta INEC Farfesa Yakubu Mahmood

‘Yan Najeriya daga sassan daban na kasar sun yi ta kiraye-kirayen a tsawaita aikin rijistar duba da cewa mutane da dama  ba su yi rijistar ba.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a Najeriya, ta ce za ta kammala aikin rijistar katin zabe a ranar 31 ga watan Yuli.

Babban kwamishina zabe a hukumar ta INEC Festus Okoye ne ya bayyana hakan bayan wani taro da hukumar ta gudanar a ranar Juma’a, yana mai cewa, daukan matakin, ya biyo bayan wani hukuncin da kotu ta yanke.

“Saboda haka, an tsawaita aikin ba da katin zabe zuwa nan da mako biyu masu zuwa, wato har sai ranar Lahadi, 31 ga watan Yuli.” Sanarwa da Okoye ya fitar bayan taron wacce aka wallafa a shafin Facebook din INEC ta ce.

‘Yan Najeriya daga sassan daban na kasar sun yi ta kiraye-kirayen a tsawaita aikin rijistar duba da cewa mutane da dama ba su yi rijistar ba.

Hukumar ta INEC har ila yau ta ce ta tsawaita sa’o’in aikin rijistar karbar katin zaben a kowace rana.

“An kuma tsawaita lokacin da ake aikin rijistar, wanda zai fara daga 9 na safe zuwa 5 na yamma a maimakon sa’a shida da aka kayyade – wato 9 na safe zuwa 3 na yamma.

“Kazalika za a rika gudanar da aikin har a ranakun karshen mako da suka hada da Asabar da Lahadi, a maimakon yadda ake yi cikin ranakun mako kadai.”

Najeriya za ta gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Sannan za a gudanar da na gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jiha a ranar 11 ga watan Maris din 2023.

XS
SM
MD
LG