Yace Baya Shakkan Bincike Don ko Makaho ya Shiga Jihar Ya san Anyi Aiki

Gwamna jihar Katsina mai barin gado Ibrahim Shema yace ba’a bin Gwamnati jihar ko sisin kwabo, kuma zai bar kusan Naira miliyan dubu hudu a asusun jihar, don haka yace baya shakkan bincike.

Gwamnan ya yi wannan furushi ne a hira da wakilin muryar Amurka, Nasiru Adamu Elhikaya, a babban birnin tarayya Abuja.

Yace “ a kwanakin baya an ce hukumar kanana hukumomin jihar Katsina bata da ko kwabo, amma wanna karya ne tunda gashi yanzu na fada maka mu saki Naira milyan dubu takwas da dari biyar ga kananan hukumomi toh daga sama suka fado kudin in babu su.”

Ya kara da cewa “har bashi aka ce ya karbo amma ya fadi cewa idan har haka ne a buga a jarida cewa ga inda na ciwo ga kuma adadin abun da na ciwo, sai aukin cewa an ciwo bashi kuma ba’a yi aikin ba toh ko makaho ya shiga jihar Katsina dai yasan anyi aiki.”