Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yana Tsoron Halin da Jama'a Zasu Shiga


Najeriya 'yan gudun hijira
Najeriya 'yan gudun hijira

Anyi kira ga Gwamnatin tarayyar Najeriya, da ta hada kai da Gwamnatin Kamaru, domin a samawa 'yan karamar hukumar Kalabalge sansani a wuri mafi kusa da inda suka fito da kuma samarmasu abinci dakuma tsaron da yakamata.

Tsohon shugaban karamar hukumar ta Kalabalge Babagana Malarima, ne ya furta haka ga wakiliyar Muryar Amurka, Madina Dauda, a Abuja lokacin da jagoranci wata tawagar 'ya'yan karamar hukumar zuwa Majalisar kasa a Abuja, domin kai kukansu.

Yace fiye da mutane dubu arba'in ne ke bukatar taimakon gaggawa, a karamar hukumar, yana mai cewa tilas a dauki matakin gaggawa na taimakon jama'ar karamar hukumar saboda 'yan kungiyar Boko Haram, sun raba su da garuruwan su wanda hakan ya tilasa masu barin kayayyakin abincinsu.

Ya kara da cewa yana tsoron halin da jama'ar zasu shiga indan har damunar bana ya sauka jama'a basu samu damar komawa gidajensu ba.

XS
SM
MD
LG