Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanonin China Na Neman Bata Sana'ar Rini


Kananan 'Yan Kasuwa
Kananan 'Yan Kasuwa

Sana’ar rini na fuskantar wasu kalu bale, tundaga shigowar wasu kamfunna kasashen china. Malam Shehu Ahmad Mai-rini, shugaban kungiyar marina ya bayyanar da wasu matsaloli da suke fuskanta tun bayan wani lokaci da wasu mutanen kasar china suka kawo musu ziyar, a wajen da suke aikin rini nasu, wanda suna ganin cewar suna aiki yanda yakamata.

A wasu lokutta na baya wadannan turawan su kawo musu ziyara wanda suka tattauna dasu a kan irin sana’ar tasu, kuma sukan kawo musu aiki suyi musu. Amma daga bisanni sai gashi sunga suma wadannan mutanen na china suna samar da irin wadannan kaya da suke samarwa kuma ma a rahusa, wanda wannan yana bata musu kasuwancinsu.

Don haka suna kira ga mahukunta dasu duba wannan matsalar su magance ta don ta haka ne kawai za’a inganta kayan cikin gida da kuma hanyar talafawa tattalin arzikin kasa. Kana kuma suna kara kira ga jama’a dasu maida hankali wajen inganta kowace irin sana’a sukeyi saboda kada kayan kasashen waje su cigaba da kwace musu kasuwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG