Rahotannin sun ambato wasu majiyoyi dake cewa matsalar da aka samu wurin masa tambayoyi ne tayi sanadiyar mutuwar Khashoggi.
Kafar labaran ta CNN mai mazauni a Amurka, ta ce majiyoyi sun gaya ma ta cewa, kuskuren da aka yi wajen kokarin tatsar bayanai, shi ne ya yi sanadin mutuwar Kashoggi. A cewar CNN, da alamar wadanda su ka tinkari Khashogji din, sun nemi su sace shi karfi da yaji ne su kai shi kasar Saudiyya don a masa tambayoyi, sai kuma abin ya zo da ajali.
Kafar ta CNN ta ce ana kyautata zaton a rahoton da Saudiyya za ta gabatar, za ta ce ba da izininta aka yi yinkurin sace Khashoggi ba, kuma za a dau matakin ladabtarwa kan wadanda ke da hannu a al'amarin.
Rahotanni sun ce ana kyautata zaton Saudiya zata bayyana cewa, abubuwan da suka faru, wanda suka yi sanadiyar mutuwarsa, an aikata ne ba tare da umarni hukumomi ba kuma za a dauki mataki a kan wadanda suka aikata danyen aikin.
Da safiyar jiya Litinin, shugaban Amurka Donald Trump, yace akwai yiwuwar miyagun masu kisa sun kashe shi.
"Ba zamu bar komai a rufe a kan wannan batu ba. Yace Sarkin ya musunta cewa ba shi da masaniya a kan kisan, kuma tana yiwuwar bai sani ba. Ba zan ari bakinsa in ci masa albasa ba, amma dai ina gani wasu muggan masu kisa ne suka aikata, amma wa ya san gaskiyar? Zamu yi kokari mu kai ga karshen wannan batu nan ba da dadewa ba."
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Sarki Salman na Saudi ya gaya masa a wata tatattaunawa da su ka yi ta tsawon minti 20 ta wayar tarho jiya Litinin cewa shi bai da masaniya kan abin da ya faru da Khashoggi, wanda aka san shi da yawan caccakar Yarima Mohammded bin Salman.
An dai ga Khashoggi a faifan bidiyo yana shiga karamin ofishin jakadancin Saudiyya makonni biyu da su ka gabata, amma tun bayan nan ba a sake ganinsa ba.