Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci gaba Da Binciki Inda Dan-Jarida Khashoggi Yake


Ana dai ci gaba da gudanar da bincike akan bacewar wani dan jaridar kasar Saudi Arebiya a babban birnin Santanbul.

Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya tace hukumomi zasu gudanar da bincike a karamin ofishin jakadancin Saudi Arebiya dake Santanbul, biyo bayan bacewar wani Dan-Jaridar kasar Saudiyya, Jamal Khashoggi.

Wata sanarwar da ma’aikatar ta Saudiyya ta fitar, ta nuna alamun a shirye take ta bada hadin kai, amma dai ba a tabbatar da lokacin da za a soma gudanar da binciken ba.

Ba a sake ganin Mr. Khashoggi ba tun bayan shigar shi ofishin a makon da ya gabata, hukumomin Turkiyya sunce an kashe shi a cikin ofishin. Amma gwamnatin Saudi Arebiya, tace ya bar ofishin lafiya.

Duk da haka, shugaban kasar Turkiyya Tayyip Erdowan, yace akwai bukatar Saudi Arebiya, ta bada bayanai gamsassu na cewar ya fita daga ofishin, a ranar Talatar makon jiya, a lokacin da yaje don karbar takardun auren shi, da yake shirin yi da wata ‘yar kasar Turkiyyar. Matar da zai aura Hatice Sengiz, tace ta jira shi a bakin ofishin amma bai fito ba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG