Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamar Agogon Khashoggi Ya Dau Yadda Aka Kashe Shi


Jamal Khashoggi
Jamal Khashoggi

A wani al'amari mai ban al'ajibi, rahotanni na nuna cewa dan jarida Jamal Khashoogi ya kunna na'urar daukar sauti da bidiyon agogonsa kafin ya shiga ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyya, inda ake tsammanin an kashe shi.

Kafofin yada labarai sun ce mai yiwuwa dan jaridar nan na kasar Saudiyya mai suna Jamal Khashoggi, ya kunna rikodar agogon Apple dinsa ya nadi yadda aka kashe shi.

Bayanai na nuna cewa Khashoggi ya kunna wajen daukar murya na agogon nasa ne yayin da ya ke shiga karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Istanbul ranar 2 ga watan Oktoba, lokacin da ya je karbo takardun da ya ke bukata na shirye-shiryen aurensa.

Bayanai na cewa agogon na hade ne da runbun adana bayanai da hotuna, wanda ke yanar internet, mai suna iCloud da kuma wata wayar salular da ya bari wurin budurwarsa kafin ya shiga karamin ofishin jakadancin. Budurwar ta sa ta ce ta yi ta jiran Khashoggi ya fito daga cikin ginin, amma bai fito ba.

Rahotanni na nuna cewa ba kawai tambayoyin da aka yi ma Khashoggi da kuntata mada da aka yi ne agogon ya nada ba, ya nadi har yadda aka kashe shi.

Khashoggi, wanda ke zaune a Amurka, ya kan yi rubuce-rubuce a jaridar Washington Post na sukar kasar Saudiyya.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai kira Sarki Salman na Saudiyya da kansa kan wannan, abin da ya kira, "mummunan al'amarin da ya faru a Turkiyya."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG