Hukumomi a nan Amurka sun gurfanar da wani matashi mai shekaru 21 da haihuwa gaban kotu su na tuhumarsa da yunkurin kashe shugaba Barack Obama ko wani ma’aikacinsa, bayan da aka zarge shi da yin harbi kan fadar White House a makon da ya shige.
Oscar Ramiro Ortega-Hernandez ya bayyana a karon farko gaban wata kotun tarayya jiya alhamis a Jihar Pennsylvania. An tsare shi cikin wani hotel a jihar ran laraba bayan da wani ya gane shi daga hotunansa da aka yi ta rarrabawa.
Za a maido da Ortega-Hernandez, dan asalin Jihar Idaho, zuwa nan Washington domin fuskantar wannan tuhuma a kotu. Idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar hukumcin daurin rai da rai a kurkuku.
Rahotannin kafofin labarai sun ce Ortega-Hernandez ya tsani shugaba Obama a can cikin zuciyarsa.
Rundunar tsaron dake kare shugaban kasa da manyan jami’an gwamnati ta ce harsasai biyu sun fada kan fadar White House, ciki har da guda da ya huda gilashin farko kafin gilashi na biyu mai sulke a jiki ya tsare shi a jikin wata taga.
Shugaba Obama da mai dakinsa Michelle ba su gida a lokacin da wannan lamarin ya faru ranar jumma’a.
Hukumomi sun fara farautar Ortega-Hernandez a bayan da suka gano alakarsa da wata motar da aka yasar ranar jumma’ar dauke da bindiga a ciki. An bayyana shi da cewa dan jinsin Hispaniyola ne, kuma ‘yan’uwansa sun kai rahoton bacewarsa tun ranar 31 ga watan Oktoba.