Tsoho Ministan sifiri,Barrister Abdullahi Idris Umar, ya musanta ikirarin daya daga cikin ‘yan kwamitin gudanarwa na hukumar Jiragen kasa, Barrister Abdullahi Jalo, kan kudi, dala miliyan dubu 1,500, na aikin shifida layin dogo, daga bukatar shugaba Buhari, ya yiwa ma’aikatar kudi da tayi bayanin yadda aka karkatar da wadannan makudan kudaden da aka karbo lamuninsu daga wani Banki a kasar China, dan aikin shinfida layin dogon da bayanai suka nuna cewa yanzu saura dala miliyan 400,a asusun Gwamnati.
Daya daga jami’an hukumar jiragen kasan da aka rushe barrister Abdullahi Jalo, wanda har ila yau shine mataimakin kakakin jam’iyyar PDP, mai adawa yace su dai basu da masaniyar yadda aka karkatar da kudaden.
Da yake maida martini ta bakin mai taimaka masa ta fuskar labaru Muhammad Amadi, tsohon Ministan sifirin tsohon Ministan sifirin Barrister Idris Umar, yace Jalo, na neman bata masa suna ne.
Da alamu dai bincike zai ci gaba kan wadannan kudade da gano gaskiyar inda suka makale.