Masana lamarin tsaro sun bayyana cewa idan tura ta kai bango, akan dauki kowane irin mataki muddin ana sa ran zai kawo sauki ga matsalar rashin tsaro.
Wannan bai rasa nasaba ga yadda gwamnoni a yankin Arewa ke kakaba dokoki a jihohinsu, don ganin an samu mafita.
Kwamishinan yada labarai na jiha Sokoto Isa Bajini Galadanci ya ce gwamnatin jihar ta bi takwarorinta wadanda suka saka irin wadannan dokokin.
Jihar ta Sokoto ta hana daukar mutum uku akan babura da kan keke-napep a duk fadin jihar.
Sauran dokokin sun hada da hana zirga-zirga daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe a cikin gari da kuma 6 zuwa 6 a yankunan da ke da matsala.
Sannan an hana kasuwancin dabbobi a garuruwa masu matsalar tsaro, da hana motoci shiga daji su dauko itace, da cinikin babura da taba-jiki a yankunan da ke da matsalar.
Masana lamurran tsaro na ganin cewa wadannan dokokin sun yi amma idan suka dauki dogon lokaci wata matsala na iya sake kunno kai.
Wadannan dokokin sun fara aiki daga daya ga watan Satumba, sai dai kuma an yi sassauci ga ma'aikatan da ke ayukka na musamman.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5