Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakin Rurrufe Al'amura Da Hanyoyi A Jihohin Da Ke Fama Da Matsalar Tsaro


Motar Sulke Da Yan Bindiga suka kona a Zamfara.
Motar Sulke Da Yan Bindiga suka kona a Zamfara.

Wasu Gwamnatocin jihohin Arewacin Najeriya musamman wadanda suka fi fama da ayukan ‘yan bindigar daji, sun soma kafa dokokin rurrufe al’amura a jihohinsu, a zaman wata hanyar yaki da ‘yan ta’adda.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya kafa dokar rurrufe wasu manyan tituna da kasuwanni a jihar, a kokarin samo bakin zaren warware matsalar tsaro da ke ci gaba da karuwa a jihar.

Wata dokar gwamnati da gwamnan ya fitar ta bayyana rufe zirga-zirga kan babban titin Jibiya zuwa Gurbin Baure da na Kankara zuwa Sheme, inda aka umarci matafiya yankunan da su yi amfani da babban titin da ke zuwa Funtuwa.

To sai dai dokar ta ba da dama ne kawai ga motocin daidaikun mutane da ba na haya ba da su bi hanyoyin, amma kuma ta haramta bin manyan motoci da kuma motocin da ke dauko itace daga jeji baki daya.

Gwamnan jihar Katsaina, Aminu Bello Masari (Twitter/@GovernorMasari)
Gwamnan jihar Katsaina, Aminu Bello Masari (Twitter/@GovernorMasari)

Har ila yau dokar ta kuma rurrufe dukkan kasuwannin dabbobi a kananan hukumomin mulki 14 na jihar, da suka hada da Jibiya, Batsari, Safana, Danmusa, Kankara, Malumfashi, Charanchi, Mai’aduwa, Kafur, Faskari, Sabuwa, Baure, Dutsinma da Kaita.

Haka kuma dokar ta haramta sufurin manyan motocin daukar dabbobi daga cikin jihar ta Katsina zuwa ko wane sashe na Najeriya.

Dokar ta kuma haramta mutane 3 hawa babur daya, ko fiye da mutane 3 a cikin a daidaita sahu wato Keke-Napep, a yayin da kuma aka haramta sayar da Babura taba-jiki a kasuwar Charanchi.

Gwamna Masari ya kuma haramta sayar da man fetur a cikin galan ko jarka, yayin da aka hana zirga-zirgar babura da a daidaita sahu daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe a babban birnin jihar, da kuma karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe a kananan hukumomin da ke fama da ayukan ‘yan bindiga.

Daga yanzu kuma gidajen mai ba za su sayar da mai ga masu galan ko jarka ba, haka kuma ba za su sayar da man da ya zarta kudi naira 5,000 ba ga kowane abin hawa a kananan hukumomin da ke fama da ayukan ‘yan bindiga.

To sai dai kuma dokar ta kebe wasu ma’aikata na musamman, kamar ma’aikatan kiwon lafiya, jami’an tsaro da ‘yan jarida, da za su iya fita ko amfani da ababen hawa a lokacin haramcin.

Masari ya ce ya kafa dokar ne bisa tanadin sashe na 176, karamin sashe na 2 na kundin tsarin mulkin Najeriya, da ya ba shi karfin iko kafa dokar sakamakon kalubalen tsaro, wadda kuma ta soma aiki daga ranar 31 ga watan Agusta.

Wannan dai na zuwa ne ‘yan kwanaki kalilan bayan da takwaransa na makwabciyar jihar Zamfara, Bello Matawalle, shi ma ya ba da sanarwar kafa dokoki kusan iri daya da na jihar ta Katsina.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Gwamnatin Zamfara)
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Gwamnatin Zamfara)

To sai dai a jihar Zamfara, gwamnati ta rurrufe dukkan kasuwannin da ke ci mako-mako a duk fadin jihar.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa yanzu haka gwamnonin sauran jihohin yankin, kamar Kaduna, Sokoto, Kebbi da Naija, duk suna nan suna shirin kafa irin wannan dokar a jihohinsu, ta yadda lamarin zai kasance na bai daya a yankin mai fama da kalubalen tsaro.

Wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da ayukan ‘yan bindiga, da suka hada da kai hare-hare, kisan jama’a da satar mutane domin karbar kudin fansa suke kara ta’azzara a yankin,

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG