Kawo yanzu mutane 31 suka rasa rayukansu kuma mai yiwuwa adadin ya karu yayin da ma’aikatan ceton rayuka suka isa yankin da wutar ta lakume. Babban jami’in ‘yan sandan arewacin California ya bayyana cewa, har yanzu ba a san inda mutane dari biyu da ishirin da takwas dake zaune a wurin suke ba.
Dubban mutane sun fice daga gidajensu domin ceton rayukansu, ba tare da sun iya daukar ko allura ba.
Hukumomi sunce an shawo kan kashi ishirin da biyar cikin dari na wutar dajin a daya bangaren California yayinda a daya bangaren kuma aka iya kashe kashi goma cikin dari na wutar kawai.
Sama da ma’aikatan kwana-kwana dubu takwas ne suke kokarin kashe wutar dajin a kudanci da kuma arewacin jihar California. Wutar dajin ta tashi ne sakamakon rashin ruwa da kuma iska mai karfi da ake fuskanta.
Jami’ai sunce wutar dajin ita ce mafi muni a tarihin jihar, kuma ta uku mafi muni a tarihin Amurka.