Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ziyarar Da Donald Trump Ya Ke a Faransa


Shugaban Amurka Donald Trump ya soke ziyarar da aka shirya zai kai wata makabartar Amurka dake wajen birnin Paris jiya Asabar, a ziyarar da ya kai Faransa domin bikin tuna cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na ‘daya.

A wata sanarwa da fadar White House ta fitar, na cewa an soke ziyarar da shugaban zai yi ne saboda wasu matsaloli da aka fuskanta sanadiyar rashin kyawun yanayi.

Maimakon haka, wata tawagar jami’an gwamnatin Amurka da shugaban ma’aikatan fadar White House John Kelly ya jagoranta, sun ziyarci makabartar domin girmama Amurkawa kusan 2,300 da suka mutu a yaki kuma aka binnesu can.

Yau Lahadi shugaba Trump zai hadu da sauran shugabannin kasashen duniya da dama domin gudanar da hidimomin ranar tuna muhimmiyar ranar cimma yarjejeniyar zaman lafiya da kasashen suka yi na kawo karshen yakin duniya na farko.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG