Wike Ya Kwace Filayen Buhari, Abbas Da Akume A Abuja

Ministan Abuja, Nyesom Ezenwo

Kwacewar ta shafe wasu mashahuren mutane da kamfanoni 759 dake yankin Maitama II ta birnin Abuja, saboda rashin biyan kudin takardun mallakar filayen.

Ministan babban birnin tarayyar Najeriya ya kwace filaye mallakin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

Haka kuma, kwacewar ta shafe wasu mashahuren mutane da kamfanoni 759 dake yankin Maitama II ta birnin Abuja, saboda rashin biyan kudin takardun mallakar filayen.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar kula da birnin tarayyar ta fitar, kuma mashawarcin ministan Abuja na musamman, Lere Olayinka, ya rabawa manema labarai.

A wata sanarwar ta daban, ministan ya kuma yi barazanar kwace karin filaye mallakin fitattun ‘yan Najeriya saboda bashin kudaden takardun mallakar filayen da ake bin su, matukar suka kasa biya cikin makonni 2.

Kwace filayen da ministan ke yi na zuwa ne watanni bayan ya yi ta rokon mazauna birnin tarayyar, musamman wadanda ke zaune a manyan unguwannin birnin, su biya bashin kudaden da hukumar kula da birnin ke bin su ko kuma su fuskanci yiyuwar kwace filayen nasu.