Shugaban hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO, yayi kashedi a kan dabarun amfani da wata hanya daban a yaki da cutar coronavirus cewa bai dace ba.
A wurin wani taron manema labarai a Geneva a jiya Litinin, babban darektan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, yace jami’an kiwon lafiya su maida hankali wurin amfani da maganin rigakafi kadai amma ba wata hanyar da zata jefa jama’a cikin hadarin kamuwa da cutar.
Hanyar yaki da cutar a kaikaice, ana amfani da ita ne a lokacin da galibin jama’a suke da kariya daga cuta saboda an kai ga cimma babbar kariya tsakanin jama’a.
Ba a taba amfani da yaki da cuta a kaikaice a matsayin dabarun yaki da barkewar annoba ba a tarihin kiwon lafiyar jama’a. Hanya ce mara inganci a kimiyance da kuma bisa tsarin yaki da cuta mai yaduwa inji Tedros.
WHO tayi kiyasi cewa kimanin kashi goma cikin dari a duniya sun kamu da coronavirus. Har iyau ba a san adadin mutanen da suke bukata wannan hanya ta yaki da cutar a kaikaice.