Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu Kamuwa Da COVID-19 a Rana Ya Karu a Duniya


Wasu masu kula da masu cutar COVID-19 a Spain, Ranar 9 ga watan Oktoba 9, 2020.
Wasu masu kula da masu cutar COVID-19 a Spain, Ranar 9 ga watan Oktoba 9, 2020.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce an samu sabon adadi na yawan wadanda ke kamuwa da cutar coronavirus a duk fadin duniya a rana guda – wanda ya kai 350,000.

Yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’a, shugaban sashen kula da daukan matakan gaggawa na hukumar, Michael Ryan ya ce, duk da cewa, cutar ta COVID-19 na ci gaba da karuwa a duniya, “har yanzu babu wata maslaha” kan yadda za a shawo kan cutar.

Ya kuma jaddadawa cewa, akwai bukatar gwamnatoci su kare rukunan mutanen da ke da hadarin kamuwa da cutar.

Kididdiga ta nuna cewa, kusan kashi uku cikin adadin yawan masu kamuwa da cutar a rana guda, daga nahiyar turai ne – inda adadin ya kai mutum dubu 109.

Sama da mutum miliyan 36.8 aka tabbatar cutar ta COVID-19 ta harba a duk fadin duniya, sannan sama da mutum miliyan daya ne suka mutu, a cewar cibiyar tattara bayanai kan cutar ta Johns Hopkins.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG