Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Mutum Miliyan 36.5 Suka Kamu Da COVID-19 a Duniya


Mutum fiye da miliyan 36.5 ne suka kamu da coronavirus, yayin da cutar ke ta bazuwa a duniya baki daya, a cewar kididdigar Cibiyar Bayar da bayanan cutar Coronavirus ta Johns Hopkins. Kasashen Amurka, Indiya da Brazil suna kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar.

Ma’aikatar lafiya ta Indiya ta ce mutane sama da 70,000 suka kamu da cutar a cikin awanni 24 da suka gabata. Amurka tana da wadanda suka kamu da cutar sama da miliyan 7.6 kuma sama da mutane 212,000 ne suka mutu.

Indiya na da kusan miliyan 7 da suka kamu da cutar, sannan sama da 106,000 ne suka mutu, yayin da Brazil ke da sama da mutane miliyan 5, da kuma mutuwar mutane kusan 149,000.

Rasha ta ba da rahoton mutune 12,126 ne wadanda suka kamu da cutar a ranar Litinin, wanda ya kawo jimillar mutane 1,272,238 wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar. Wasu jami'ai sun ce mai yiwuwa a sake sanya sabon takunkumi.

Bangarorin kiwon lafiya dabam-daban a Washington, DC, da jihohin Maryland da Virginia sun aika wasiku jiya alhamis, suna kira ga ma’aikatan da suka yi aiki a Fadar White House a cikin makonni biyu da suka gabata, ko kuma suka halarci wani taro na ranar 26 ga Satumba a Lambun Garden Rose "da su tuntube sashin hukumomin lafiya na gida domin tambayoyi ko jagoranci akan yiwuwar su kebe kansu. ”

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG