A karon farko, hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta amince da allurar rigakafin cutar kyandar biri gabanin a kammala gwaji akanta.
Sanarwar na zuwa ne bayan isar rukunin farko na allurar rigakafin MVA-BN jamhuriyar dimokiradiyar Congo, inda cutar tafi kamari.
An samu kusan mutane dubu 22 da suka kamu da cutar congo sannan ta hallaka wasu 716 tun cikin watan Janairun da ya gabata.
Izuwa yanzu dai, tarayyar turai ta tura allurar rigakafi dubu 200 zuwa jamhuriyar dimokiradiyar Congo, tare da wasu dubu 50 daga Amurka.
Cutar kyandar biri (Mpox) wacce a da ake kira da monkeypox a likitance, nau’in kwayoyin cutar virus da dabbobi ke yadawa mutane amma mutum ma na iya yadata ga sauran mutane mutakar akwai mu’amala ta kusa.
Cutar wacce ke haddasa zazzabi da ciwon gabbai da kuraje masu kama da kazuwa, na iya zama mai matukar hadari a wasu lokutan.
WHO ta wallafa a shafinta na X a yau juma’a cewa, ana sa ran samun alluran rigakafin ya hanzarta yakin da ake yi da annobar dake bazuwa a nahiyar Afirka.
Ku Duba Wannan Ma UNICEF, WHO DA CDC Suna Hadin Gwiwar Samar Da Rigakafin Kyandar BiriA cikin sanarwar shugaban hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus yace, “amincewa da rigakafin gabanin kammala tantanceta wani muhimmin mataki ne a yakin da muke yi da cutar kyandar biri, a yunkurin da muke yi na shawo kan barkewarta a afrika a halin yanzu, dama nan gaba.”