Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Kamu Da Cutar Kyandar Biri A Najeriya Ya Kai 53 - NCDC


Wani mutum da ake yi wa allurar rigakafin cutar kyandar biri
Wani mutum da ake yi wa allurar rigakafin cutar kyandar biri

A wata sanarwa da take fitarwa mako-mako, hukumar ta NCDC a rahotonta na mako na 35 ta ce an samu karin mutum biyar da cutar ta harba.

Hukumar da ke yaki da yaduwar cututtukaa Najeriya ta NCDC ta ce yawna mutane da suka kamu da cutar kyandar biri ya kai 53.

A wata sanarwa da take fitarwa mako-mako, hukumar ta NCDC a rahotonta na mako na 35 ta ce an samu karin mutum biyar da cutar ta harba.

A Rahotonta na mako na 34, NCDC ta ce mutum 48 cutar ta harba.

A mako na 33, adadin mutanen da suka kamu da cutar 40 ne.

Kusan makonni biyu da suka gabata Amurka ta ba Najeriya allurar rigakafin cutar ta kyandar biri, hakan ya sa ta zama kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta samu tallafin rigakafin.

“Allurar rigakain guda 10,000 za a raba su a jihohi biyar domin kare wadanda suke cikin hadarin kamuwar da cutar.

A wannan mako Amurka ta ba Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo tallafin allurar rigakafi wacce it ace kasar da cutar ta fi Kamari.

“Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na aiki da sauran abokan hulda don ganin an kara fadada raba allurar rigakafin a sassan Afirka.” WHO ta ce.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG