Whatsapp ya ‘kara wata manhajar da zata ke sarkake sakonnin da masu amfani da wayar iphone ke ajiyewa a ma’ajiyarsu ta iCloud, a wani yunkuri na kaucewa masu kutsen satar bayanai.
A shekarar da ta gabata ne Whatsapp ya kirkiri manhajar da zata ke kare sakonnin mutane da tabbatar da cewa sakonnin sun kai ga mtuanen da aka aikewa, amma sai gashi a baya bayan nan akan iya ajiye sakonnin mutanen da suke amfani da wayoyin iphone, wanda hakan ka iya jefa sakonnin hannun da bai kamata ba.
Wayoyin iphone na amfani da iCloud wayen ajiye dukkan bayanan da ke cikin waya wanda suka hada da sakonnin da mutane ke aikawa, sai dai kuma idan wani ya sami ‘danmukulli na musamman da ake kira decryption key, zai iya samun dukkan bayanan mai amfani da wayar iphone.
Abin tsoro anan shine hukumomin tsaro zasu iya umartar kamfanonin waya da su mika bayanai kan wani da suke bincika, haka kuma masu kutse kansu na iya samun bayanan mutane cikin sauki.
Wannan manhaja da whatsapp ya ‘kara zata taimaka wajen karfafa tsaron sakonnin masu amfani da wayar iphone ko amfani da na’urorin kamfanin Apple.
Your browser doesn’t support HTML5