Wayne Rooney Ya Sagale Takalmin Taka Leda

Wayne Rooney

Jagoran tawagar ‘yan wasan kasar Ingila, Wayne Rooney, ya bayyana ajiye takalman taka ledarsa wa kungiyar kwallon kafa ta kasarsa ta Ingila, bayan da ya shafe shekaru, goma sha hudu, yana murza mata leda.

Rooney, mai shekaru talatin da daya da haihuwa ya je kungiyar kwallon kafa ta Kasar Ingila a lokacin yana matashi mai shekaru 17, ya bayyana hakan ne a jiya,

Dan wasan wanda yazamo dan wasan da yafi kowa zurara kwallo a tarihin kungiyar ta Ingila, ya jefa kwallaye har guda 53 a raga, a wasannin 119.

Kafin zuwa babban kungiyar kwallon kafar kasar, ya buga wasannin a bangaren kungiyar matasar Ingila ‘yan kasa da shekara 15, 17 da kuma 19, tun daga shekara ta 2000 har zuwa 2003.

Wayne Rooney, yace ya ajiye takalman ne domin ‘yan wasan, masu tasowa damar bada tasu gudumawar wa kasar. ta fannin kwallon kafa.

Ya kuma ce yanzu zai maida hankalinsane akan kungiyarsa ta Everton, inda ya dawo daga Manchester United, a bana bayan ya shafe shekaru Goma sha uku da barinta.

Rooney yayi fice wajan zurara kwallo a raga, inda a satin da ya wuce ya jefa kwallon farko a wasan da Everton da Manchester City, sukayi na gasar Firimiya lig na 2017/18 a wasan mako na biyu inda aka tashi 1-1

Kuma shene dan wasan da yafi kowa jefa kwallo a tarihin Manchester United da kuma Firimiya lig na kasar Ingila,

A kwana kwanan nanne, mai riki da tawagar kungiyar kwallon kafa ta Kasar Ingila, mai suna Southgate, ya bayyana sha'awarsa na cigaba da amfani da wayne Rooney, a kungiyar kwallon kafar kasar.

Your browser doesn’t support HTML5

Wayne Rooney Ya Sagale Takalmin Taka Leda 4'42"