Sabon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Romelu Lukaku, tauraron sa ya fara haskakawa a Firimiya lig ta 2017/18, a kasar Ingila,
Shidai Lukaku, ya dawo kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a farkon kakar wasan bana, daga tsohowar kungiyarsa ta Everton, akan zunzurutun kudi har fam miliyan £75.
A yanzu haka dan wasan ya jefa kwallaye har guda ukku a wasanni biyu da ya buga wa Manchester bangaren Firimiya lig na bana,
A wasan da Manchester united tayi tsakaninta da Westham united, ranar lahadi 13/8/2017 a makon farko na Firimiya lig,
.
Dan wasanne ya fara jefa kwallon farko acikin mintuna na 33 da kuma kwallo ta biyu a minti na 53 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci,
Daga bisani Antonia Martial, ya saka kwallo ta ukku sai Paul Pogba, ya zurara ta hudu haka dai aka tashi wasan 4-0,
A wasa na biyu tsakaninta da Manchester da Swansea City inda Manchester United ta lallasa ta da kwallaye 4-0 a Old Trafford, Romelu Lukaku, tauraransa ya cigaba da haskakawa inda ya sake jefa kwallo ta biyu a ragar Swansea, a mintuna na 80.
Dan wasan baya Manchester Bailly, shi ya fara jefa kwallon farko a minti 45 ana dab da tafiya hutun rabin lokaci. Shima Pogba, ya sake saka kwallon ta ukku daga bisani Antonia Martial, ya saka kwallo ta hudu. hakan ya bada dama ga kungiyar ta Manchester united, ta cigaba da zama a saman teburin Firimiya a mako na biyu da maki shida.
Sai Huddersfield town, itama da maki shida, a matsayi na biyu,
Westbromwich tana mataki na ukku da maki shida.
Ranar Asabar 26/8/2017 kungiyar ta Manchester united zata karbi bakuncin Leicester City a wasan mako na ukku a gasar Firimiya lig 2017/18.
Facebook Forum