Hukumar kwallon kafa ta duniya, (FIFA) ta fitar da jerin sunayen masu horas da ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, domin zabar mutundaya daga cikinsu a matsayin wanda yafi taka rawar gani a bana, ta bangaren koyar da ‘yan wasan kwallon kafa na maza, (Best FIFA Men's Coach).
A cikin jerin sunayen akwai Zinedine Zidane, na Real Madrid wanda ya lashe Kofin zakarun nahiyar Turai (UCL) da La-Liga 2016/17 na Kasar Spain, da kuma Club World Cup, Sai Jose Mourinho na Manchester United da ya samu nasarar cin kofuna guda uku a shekararsa ta farko a Manchester.
Akwai Antonio Conte na kungiyar Chelsea wanda shi kuma ya lashe kofin Firimiya lig 2016/17 na kasar Ingila.
Sauran jerin sunayen sun hada da Kocin Manchester City Pep Guardiola, Diego Simeone, na Atletico Madrid, sai Massimiliano Allegri na Juventus, akwai kuma mai horas da kungiyar kwallon kafa ta kasar Jamus, Joachim Low, da Tite, na kasar Brazil, da dai sauransu.
Za'a cere sunayen mutum uku daga cikinsu wanda zasu fafata wajan lashe wannan kyautar a yayin taro da za'ayi na jama'a, wanda zai gudana tsakanin ran 21/8/2017 ko kuma 7/9/2017.
Jagororin ‘yan wasa watau (Captain) na kungiyoyi kwallon kafa da kuma wakilin ‘yan jaridu na duniya ne zasu jefa kuri'ar wajan fidda gwarzon a bana.
Facebook Forum