Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Real Madrid Ta Taka Rawar Gani


Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ta lallasa babbar abokiyar hamayyarta Barcelona da kwallaye 2-0 a karawarsu ta biyu a wasan karshe na cin kofin Spanish Super Cup, na bana a ranar laraba 16/8/2017 a filin wasa na Santiago Bernabeu, mai daukar mutune dubu 85,454.

Dan wasan Madrid Marco Asensio, ne ya jefa kwallon farko a ragar Barcelona, cikin minti hudu da fara wasan, daga bisani dan wasan gaban Real Madrid Kareem Benzema, ya zurara kwallo ta biyu a komar Barcelona, a minti na 39 kafin tafiya hutun rabin lokaci, haka dai wasan ya tashi da kwallaye 2-0.

A haduwarsu ta farko da sukayi ranar lahadi 13/8/2017 a Camp Nou, kungiyar ta Real Madrid, ta doke Barcelona, da kwallaye 3-1 inda ta hada jimilar kwallaye 5 -1 a dukka wasannin biyu da su kayi.

Hakan ya ba kungiyar ta Madrid nasara ta lashe kofin Spanish Super Cup, na bana.

Real Madrid, tayi rawar gani a wasan inda ta taka leda fiye da Barcelona, duk da cewar ba shahararren dan wasan gabanta Cristiano Ronaldo, sakamakon dakatar dashi da akayi a wasannin 5 bisa rashin da'a da ya nuna wa alkalin wasa, a karawar farko da sukayi da Barcelona.

Itama a nata bangaren Barcelona, dan wasanta Andres Ineista, bai samu damar buga wasanba saboda jinya da yake yi.

A ranar Jumma'a 18/8/2017 za'a fara gasar cin Kofin laliga na shekara 2017/18 a kasar Spain, inda ranar lahadi 20/8/2017 Barcelona, zata karbi bakuncin Real Betis, ita kuwa Real Madrid, zata je bakuncine a gidan Deportivo.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:46 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG