Wata sabuwar badakalar siyasa ta kunno kai a jahar Kebbi a yayin da majalisar dokokin jahar ta aika wa gwamnan takardar yunkurin tsige shi daga mukamin sa, kwanaki 29 kacal kafin karewar wa’adin aikin sa.
Lamarin ya biyo baya ne kwana daya bayan tsige tsohon kakakin majalisar jahar tare da wasu shugabannin majalisar a watan Nuwambar da ya gabata, inda suka tattaru da sauran takwarorin su wadanda suka sauya sheka daga jam’iyar PDP zuwa APC da ta lashe zaben gwamnan jahar.
‘Yan majalisar dai sun tsige sabon kakakin majalisar Alhaji Ibrahim Shalla ne suka kuma mayar da tsohon kakakin majalisar Aminu Musa Jega bisa kan mukamin sa.
A rahoton Murtala Faruk Sanyinna, shugaban ya yi Karin bayanin cewa daya daga cikin dalilan da suka sa daukar matakan sun hada da “wasu takardun bada umurnin yin wasu ayyukan da basu kamata ba domin bata dukiyar jahar Kebbi ne a inda bai kamata ba. Kuma wadannan kudade basu cikin lissafin kudaden da aka ce an kashe a jahar, da kudin da aka ce an biya malaman makaranta da kuma na harkar tsaron jahar”.
Jam’iyar PDP a jahar ta mayar da martanin cewa, bai kamata su fuskanci lamuran ta wannan haryar ba domin sun ci zabe. Alhaji Muntari Sarki wanda yana daya daga cikin manyan jiga jigan jam’iyar PDP ya yi karin bayanin cewar “dukkan ‘yan majalisar ‘yan PDP ne amma ganin cewa bukatun su basu biya a PDP ba ne yasa suka kaurace zuwa APC”.
Your browser doesn’t support HTML5