Hukumar ta musanta zargin ne a wani taron manema labarai da tayi a hedkwatarta dake Sokoto.
Hadarin motar da ya auku a Argungu ya lakume rayuka hudu abun da ya zama musababin kona ofishinta dake garin.
Daniel Shayi kwamandan hukumar a jihar Kebbi ya bayyana cewa hadarin ya auku ne gaf da wurin da jami'ansa ke sintiri. Amma babu wani daga cikinsu da yayi kokarin kama mai babur din da suka yi hadari da mota.
Yace abun da ya faru shi ne mai babur yana kan tafiya zai zo ya shiga wata kwana amma bai waiwaya baya ba. Yana kokarin yin hakan sai kuma ga mota tana zuwa da gudu dauke da mutane bakwai. Mai mota yayi kokarin ya kaucewa mai babur sai motar ta kwace daga hannun mai tukinta har ta samu hadari inda nan take mutane uku suka mutu daya kuma ya karasa a asibiti.
Daniel Shayi ya musanta zargin cewa kokarin kama mai babur din da jami'ansa suka yi ya rudar da shi da kuma direban motar. Ya rabawa manema labarai faifan bidiyon hadarin da abubuwan da mai babur din ke fada.
Shi ma mai babur din ya tabbatar cewa babu wanda yayi kokarin tsayar dashi. Yace ko da ya shiga kwanar bai ankara mota na zuwa ba sai da jami'in hukumar ya yi kokarin jawo hankalinsa amma lokaci ya kure sai motar ta bigeshi kafin ta samu hadari.
Hukumar ta tabbatar da kone ofishinta da masu bori suka yi tare da kone motoci bakwai mafi yawansu wadanda hukumar ke tsare dasu. An kuma sace babura 16 dake harabar ofishin.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.